Advertisement

Yan kunar bakin wake sun kai hari masallaci da gidajen yan gudun hijira

Mutum 18 sun mutu yayin da 29 suka jikata a harin da ya faru gidan yan gudun hijira dake wajen garin Maiduguri
Advertisement

Mutum 18 sun mutu yayin da 29 suka jikata a harin da ya faru  a garin Muna Gari dake karamaar hukumar Konduga na jihar Borno yammacin ranar laraba.

Advertisement

Kakakin hukumar yan sanda na jihar mista Victor Isuku ya tabbatar da harin a wata takarda da ya fitar ma manema labarai a garin Maiduguri.

Kakakin yace lamarin ya faru daidai karfe 6:30 na yamma yayin da wasu yan kunar bakin wake hudu suka kai harin garin dauraye da bama-bamai a jikin su.

A bisa bayanin sa, tashin bam na farko ya faru ne cikin masallaci kuma daga bisani sauran suka tashi a wurare daban-daban na yankin.

Isuku yace wadanda suka ji rauni sanadiyar harin suna samun kulawa a asibitin koyi na jami'ar maiduguri tare da asibitocin gwamnati na jihar.

Advertisement

Daga karshe kakakin ya sanar da cewa an tura wasu runduna zuwa garin domin kawar da tashin hankali a zukatan mazaunin garin.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement