Advertisement

Boko Haram ta kashe ma'aikaciyar jin kai, tayi barazanar kashe Leah Sheribu

Ta kara da cewa zuwa nan da wata daya za'a halaka ma'aikaciyar raino da unguwarzoman dake garkame a hannun su.
Advertisement

Mayakan wani karamin kungiyar Boko haram dake gudanar da aika-aikar su a yammacin Afrika ta kashe wata maaikaciyar jin kai na Red Cross da aka sace kwanan baya.

Advertisement

Mayakan sun sace ma'akaciyar cibiyar mai suna, Saifura Hussaini Khorsa, a cikin watan Maris na 2018 yayin da suka kai hari shingen sojoji a garin Rann na jihar Borno.

Kamar yadda rahotanni  suka bayyana akalla mutum takwas suka rasu sakamakon harin cikin su har da sojoji da ma'aikatan kiwon lafiya da wani likitar UNICEF.

Kungiyar ta daura alahkin kisan da tayi ga gwamnatin Nijeriya bayan da ta tura mata sakon kuma kai ga yanzu ba'a mayar da amsa ba.

A rahoton da The Cable ta fitar, kungiyar tace ta tura sakon murya ga gwamnati amma gwamnatin tayi kunnen kashi ga sako shiyasa suka tunatar jama'a ta hanyar bindige ma'aikaciyar.

Advertisement

Bugu da kari kungiyar tace zata hada da yar makarantar Dapchi daya tilo dake hannun su har yanzu.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement