Advertisement

Yan sanda sun gayyaci dan takarar gwamna kan zargin magudin jarabawa kwana uku gabanin zabe

Senator Ademola Adeleke
Senator Ademola Adeleke
Ademola Adeleke yana daya daga cikin yan takarar gwamnan jihar Osun a zaben jihar da za'a gudanar ranar asabar 22 ga watan Satumba.
Advertisement

Rundunar yan sandan Nijeriyan ta tura ma Sanata Ademola Adeleke tsammaci domin amsa zargin yin magudi a jarabawar NECO da kuma zargin bita da kulli.

Advertisement

A labarin da Channels Tv ta fitar ana zargin dan takarar da kulla makarkashiya da wasu mutane hudu yayin rubuta jarabawar a shekarar 2017.

Tsohon dan majalisar dattawa wanda zai fito karkashin jam'iyar PDP yayi suna a kasar duba da faidan bidiyo din shi yayin da yake tika rawa yake yawan mamaye kafafen sadarwa.

Hakazalika dan siyasan ya shahara sakamakon dangantarkar shi da fitaccen mawakin Nijeriya wato Davido.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yan sanda na kasa Jimoh Moshood, ya sa hannu, ana zargin Adeleke da yin zaman jarabawar NECO ta hanyar sajewa a madadin wani dalibin makarantar Ojo/Aro Community High Schoo dake jihar Osun a cikin shekarar 2017.

Advertisement

Duk da cewa dan takarar yana da shekaru 57, sanarwar ta bayyana cewa ya karyata labarin shekarun sa kamar yadda hukumar NECO ta bayyana.

Senator Ademola Adeleke on the NECO Album for students of Ojo/Aro Community High School in Osun State
Senator Ademola Adeleke on the NECO Album for students of Ojo/Aro Community High School in Osun State

An zargi Adeleke da rage shekarar haihuwar sa zuwa 1997.

Rundunar yan sanda na neman sa tare da sauran mutane hudu da ake zargin sun taimaka masa wajen aikata laifin domin su gabatar da kansu a ofishin su dake garin Abuja domin a gabatar dasu gaban kotu.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement