Jami'an yan sanda na jihar Osun suna tuhumar wani matashi mai shekaru 29 bisa ga laifin yi ma wata tsohuwa fyade har ta fita hayacin ta.
A bisa labarin da jaridar Punch ta fitar, an kama Kehinde Ariyo wanda ake zargi a garin Ilesa ranar juma'a 27 ga watan octoba.
Kwamishnan yan sanda na jihar Osun Fimihan Adeoye ya tabbatar da kama shi yayin da aka gabatar dashi a hedikwatar su dake nan garin Oshogbo babban birnin jihar.
Adeoye yace mai laifin gawurtaccen mai fyade ne kuma shiga cikin tsohuwar a asirce daidai karfe 11 na dare kuma yayi mata fyade har ta suma.
Yace tsohuwar taji rauni da dama a har ma a farji kuma an ruga da ita sibiti da lamarin ya faru amma yanzu ta fara farfadowa.
An samu labari cewa matashin yayi amfani da kusancin sa da tsohuwar wajen aikata laifin domin suna zaune a unguwa daya kuma ta kan aike shi yayi mata hidima.
Shi dai mai laifin yace lamarin ya faru ne yayin da yake cikin maye domin yaje wata biki inda ya yayi tatur da giya.
Matashin yace dani kawai yayi ba wai yayi lalatar kamar yadda ya kamata.
Yayi ikirari cewa shaytan ya rinjaye shi har aikata hakan.
Kwamishna Adeoye ya dau alkawarin gurfanar dashi bayan an gama bincike domin ya zama darasi ga sauran masu aikata laifin.