Tsohon gwamnan jihar Kano kuma daga daga cikin yan takarar shugaban kasa na jamiyar PDP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yace zai doke shugaba Buhari cikin ruwan sanyi idan ya zama dan takarar jamiyar sa a zaben 2019.
Jagoran tafiyar Kwankwasiya yace yana da darajan kwato tutar mulki daga hannun jam'iyar APC a zaben gobe.
Yana mai cewa "idan na zama gwanin PDP , ni zan zama shugaban Nijeriya".
Kwankwaso yayi ikirari cewa yana da dinbim magoya a yankin arewa yamma kuma yawan su zai karu muddin jam'iyar PDP ta bashi damar zama dan takarar ta.
Ya kuma soki gwamnati mai mulki ta APC inda yace ta gaza kawar da yunwa da rashin aikin yi da ake fama da ita a kasar.
Yayi alkawarin samad da ingantacciyar ayyukan cigaba da kuma tabbatar da tsaro tare da bunkasa harkar ilimi.
Yace zai kwatanta kwatankwacin tsarin ilimi na kyauta da yayi sanda yake gwamnan Kano idan ya zama shugaba.
Kwankwaso ya kuma yi alkawarin gina hanyoyi da gadaje domin tallafawa safarar mutane da kaya.