LASEMA sun dawo da gawar Likitan da ya kashe kansa
Kungiyar tafiyad da ayyukan gaggawa na Legas (LASEMA) a ranar Laraba ta ce, ta gano gawar Dr Allwell Orji cikin kogi a ranar Lahadi.
Mr Adesina Tiamiyu, Janar Manaja na LASEMA, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), a Legas cewa, ƴan sandan ruwa sun gano gawar a ƙarfe 4 na yamma.
“Ƴan uwansa sun bayyana gawar, haɗe da direban sa a gaban Kwamishinan ƴan sanda na Jihar Lagas, Mr Fatai Owoseni.
An miƙa gawar zuwa ga iyalin sa, yayin za a cigaba da bincike, Tiamiyu ya ce.
Janar manaja ya nuna ta'aziyya a madadin gwamnatin jihar, da kuma furta rufe binciken gawar.
NAN ta ce Orji, likita, ya je gadar third mainland tare da direbansa a ranar Lahadi, ya sauka, ya yi tsalle ya shiga cikin kogin.
Marigayin, da, na aiki a asibitin Mount Sinai a yankin surulere a Legas, ya nitse kafin taimako ya iso.
Ƴan sanda a ranar Talata sun samu wani gawa da suka zaci na Orji ne, amma iyalin sa ki ansa , da cewa ba dan uwansu bane.