Advertisement
Ma'aikatan Nijeriya zasu tafi yajin aiki
'yan kungiyar kwadago yayin da suke gudanar da gangami
NLC tace an dauki matakin zuwa yajin aikin ne bayan wa'adin da suka baiwa gwamnatin tarayya na tsawon kwana 14 domin duba lamarin albashi mafi karanci.
Advertisement
Kungiyar yan kwadago (NLC) ta sanar da cewa zuwa daidai karfe 12 na Daren ranar laraba maaikata dake fadin kasa zasu fara yajin aiki.
Advertisement
Gamayyar Kungiyar NLC da TUC sun kudura anniyar su na tafiya yajin aiki kamar yadda shiugabannin kungiyoyin suka bayyana.
Kungiyoyin sun dauki matakin ne domin nuna bacin ransu game da batun albashi mafi karanci na ma'aikata dake kasar wanda gwamnatin tarayya ta kaddamar amma bata fara aiwatar da tsarin ba.
Labarin tafiya yajin aiki ya fito ne a cikin wata sanarwa da sakataren NLC, Peter Ozo-Eson, ya sa hannu.
Sanarwar ta gargadi sauran ya'yan kungiyar dake jihohin kasar da su bada hadin kai wajen bin umarnin uwar kungiyar na tafiya yajin aiki.
Advertisement
Sai dai yajin aikin zai cigaba har zuwa lokacin da aka fitar da sabon umarni kan batun.
Advertisement
Subscribe
Sportal WhatsApp
Latest Videos
Nigeria hausa
Gobara tayi sanad in mutuwar mutum 35
11.09.2018
Advertisement
Videos
Advertisement
Advertisement
More from Pulse Nigeria
Advertisement