Advertisement

An hana musulmai saki uku lokaci guda

A cikin shekarar 2017 kotun kolin kasar ta zartar da hukuncin haramyta haka inda kuma ta nemi gwamnatin kasa da ta kafa doka kan batun.
Advertisement

Majalisar zartarwar Indiya ta amince da doka mai tsauri da ta haramta yi wa mata saki.

Advertisement

Kamar yadda Ministan doka na kasar Ravi Shankar Prasad ya bayyana  daga yanzu za'a      hukunta duk mutumin da ya yi wa matarsa saki uku lokaci guda.

A cewar ministan, majalisar zartarwar ta amince da dokar ne saboda maza na ci gaba da aiwatar da irin wannan saki duk da hukuncin da kotun kolin kasar ta zartar na haramta shi kwanan baya.

Gwamnatin India ta dade tana kokarin ganin majalisar dokokin kasar ta amince da hukuncin daurin shekara uku ga duk mutumin da ya keta wannan doka.

Sai dai 'yan hamayya na so a yi a dokar gyaran fuska ta yadda ba za a yi amfani da ita wajen musgunawa jama'a ba.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement