Advertisement

Kotu ta gyara mai zama bayan yayi wa matar sa wanka da ruwan batir

Dan sanda da ya gurfanar dashi gaban kotu yace ya nemi ya kashe matarsa ta hanyar zuba mata ruwan batir a jiki
Advertisement

A ranar litinin 11 ga watan Satumba kotun magistare dake garin Ibadan ta hukunta wani Sofiu Yahaya mai shekara 42 zuwa gidan yari bisa ga laifin neman kashe matar sa ta hanyar zuba mata ruwan batir a jiki.

Advertisement

Mrs Modinat Akani ta yanke hukunci tare da cewa Yahaya ya cigaba da zama gidan yari har sai taji shawarar da hukumar gurfanar da masu laifi na jihar zata bada.

Yahaya wanda ke zama a Oritamerin na garin Ibadan ya shiga hannun hukuma bisa ga laifi da ya danganci kisa.

A bisa biyanin da jami’in yan sanda da ya gurfanar dashi gaban kotu sufeto Sunday Fatola, Yahaya ya nemi ya kase matar sa Fatimo mai ta hanyar zuba mata ruwan batir a jiki.

Fatola yace wanda ake ma zargi ya aikata laifin a ranar 24 na watan Agusta dai dai karfe 4:00 na yamma a unguwar Oritamerin dake nan Ibadan.

Advertisement

Laifin da aikata ya karya doka cikin sashe 320 na kundin tsarin mulkin jihar Oyo.

Kotu ta daga zama kan batun zuwa 16 ga watan Nuwamba.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement