Ministan kudi Kemi Adeosun ta siffanta tsarin tonon asiri ta Whistle-blower policy a matsayin babban hanyar samun nasara a tsare-tsaren gwamnati wajen gano kudaden gwamnati da aka sace.
Ministan tace nasarar da gwamnatin Muhammadu Buhari tayi karkashin tsarin ya wuce iyakar da suke zato.
Ta sanar da haka ranar lahadi 29 ga watan octoba a wata rubuce-rubuce ta musamman datayi.
Ministan ta bayyana cewa an gano naira biliyan 11.63 (N11.63B) karkashin tsarin a cikin watan Yuni.
Ta kara da cewa an biya naira 375.8 (N375.8M) ga wadanda suka taimaka da labarai da yayi sanadiyar gano kudaden.
A isa labarin ministan tsarin da gwamnati ta kaddamar na ayana kudaden gwamnati a asusu guda yana mataimakawa sosai kuma yana taimakawa wajen bin diddigi akan yadda ake kashe kudaden.
Ministan tace a tsarin da, abu mai sauki ne a sauya asusun gwamnati zuwa mallakar mutum amma cikin wannan tsarin ayana kudi zuwa asusu guda ire-iren haka baza ta faru ba.