Advertisement

Majalisa ta bukaci Buhari ya bayyana gaban ta kan kashe-kashen dake faruwa

Ta bukaci shugaban da ya gabatar da kanshi zauren domin bada bayanin matsalar tsaro da ake fuskanta a kasar
Advertisement

Majalisar tayi wannan kiran ne a zaman majalisa da tayi yau laraba 25 ga watan Afrilu.

Advertisement

Ta bukaci shugaban da ya gabatar da kanshi zauren domin bada bayanin matsalar tsaro da ake fuskanta a kasar.

Sai dai majalisar bata sanar da ainihin ranar da shugaban zai bayyana a gaban ta. Yan majalisar sun kuma gudanar da zaben kin jin bisa gazawan jami'o'in tsaro na kasa wajen kawo karshen kashe-kashen dake faruwa a kasa.

Wannan matakin dai ya biyo bayan kudirin da Mark Gbillah, dan majalisa mai wakiltar jihar Benue ya shigar, kan kashe-kashen da ya faru a jihar sa.

Bayan muhawara da su kayi kan kudirin yan majalisar suka yanke shawarar gayyatar shugaban kasa.

Advertisement

Yan majalisar dai sun dangata rikicin dake faruwa a kasar ga gazawan shugaban kasa wajen kalubalantar jami'o'in tsaro wajen inganta aikin su.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement