Advertisement

Jaruma ta samu babban matsayi a gidauniyar Atiku

___8884121___2018___9___21___11___atikucarefdn_40985354_252425338679529_9179215723029977318_n
___8884121___2018___9___21___11___atikucarefdn_40985354_252425338679529_9179215723029977318_n
Maryam Booth ta shiga sahun sauran abokan aikin ta na masana'antar kannywood dake rike da matsayi karkashin wannan gaidauniyar.
Advertisement

Fitacciyar jaruma Maryam Booth ta samu babban matsayi a gidauniyar tsohon mataikin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar.

Advertisement

Gidauniyar Atiku Care Foundation wacce take tallafa wa mara sa galihu ta daukaka mukamin ta daga jakadiya zuwa mukamin mataimakin shugaba na  yankin arewa.

Gidauniyar ta sanar da hakan ne ta  hanyar wani sako da ta wallafa a shafin ta na kafafen sadarwa inda ta bayyana cewa matsayin zai fara aiki daga ranar juma'a 21 ga watan Satumba.

Maryam Booth ta shiga sahun sauran abokan aikin ta na masana'antar kannywood dake karkashin wannan gaidauniyar.

Wasu daga cikin fitattun jarumai da suka samu matsayi a gidauniyar sun hada da Fati Muhammad, Rashida Adamu da Abdu Boda.

Advertisement

An kafa gidauniyar ne domin taimakawa mara hali tare da nuna aikin tallafawa da Atiku Abubakar keyi ga idon jama'ar Nijeriya har da na kasashen waje.

Har ila yau gidauniyar Atiku Care Foundation ta zama cibiya da tsohon mataimakin shugaban kasa ke samu yana mu'amala da yan kasa a ko wani lungu da sako ta hanyar kafafen sadarwa da gidauniyar ta kafa.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement