Ƴan sanda sun nuna kuɗi miliyan ɗari wanda Gwamna ya bai wa maʼaikatan hukumar zaɓe INEC
Kwamitin Ƴan sanda wanda aka kafa domin bincika zaɓen Jihar Rivers wanda aka sake yii a watan Disamba 2016, sun fara bincike-binciken zargin da aka yi ma Gwamna Nyesom Wike game da cin-hanci wanda ya ba maʼaikacin hukumarʼ zaɓe, waton INEC.
A lokacin da ákê fama da wannan bincika, masu bincika sun nuna kuɗin takarda miliyan ɗari wanda ake tsamanin cêwa Wike ya aika zuwa ga maʼaikacin hukumar zaɓe (INEC) a madadin cin hanci, domin tabbatar da cêwa sun rarraba yawancin zaɓe wanda aka kaɗa zuwa Jamʼiyyar PDP.
Wike ya ƙaryata zargin da aka yi akai-akai cêwa ya yi magudi a zaɓen da aka yi, kuma ya ƙi amincewa da bincike-bincike na Ƴan sanda. A maimakon haka, ya kaffafa wani fanel domin bincika abubuwan da suka faru a lokacin zaɓe. Ya kai ƙara zuwa kotun Gwamnatin Tarayya na Abuja domin dakatar da bincika wanda aka fara yi, amma kotun sun ƙi amincewa da rokonʼsa.
Sufeto-Janar na ʼƴan sanda, Ibrahim Idris, ya sanar ma kotu cêwa Wike yana neman ya rufe sahonʼsa, da kuma asirinʼsa.
Idris ya ce hukumar bincike-bincike wanda Wike ya kaddamar, ba su da iznin bincika zaɓe wanda aka yi a Jihar Rivers.