Advertisement

Ma'aikatan jihar Kaduna basu tafi yajin aiki ba

___8909183___2018___9___27___14___NLC1
___8909183___2018___9___27___14___NLC1
Wata ma'aikaciyar jinkai na asibitin Barau Dikko ta shaida cewa basu samu sammame daga kungiyar kwadago na jihar domin tafiya yajin aiki.
Advertisement

Yayin da maaikata dake karkashin kungiyoyin kwadago ke gudanar da yajin aiki a fadin kasa, maaikatan reshin jihar Kaduna sun bijire ma matakin.

Advertisement

Kamfanin dillancin labarai (NAN) ta ruwaito cewa ma'aikata dake hukumomi dake garin Kaduna sun koma bakin aikin su duk da yajin aikin da NLC da TUC keyi.

Wakilin NAN ya ruwaito cewa ma'aikatu, bankuna, asibiti da sauran su sun bude kofa kuma ma'aikatan su suna nan bakin aiki.

Wata ma'aikaciyar jinkai na asibitin Barau Dikko ta shaida cewa basu samu sammame daga kungiyar kwadago na jihar domin tafiya yajin aiki.

A wata labari da muka fitar kun ji cewa malaman makarantar Abubakar Tattari Ali Polytechnic dake Bauchi suma sun bijire ma matakin yajin aiki da kungiyoyin kwadago suka dauka yau Alhamis 27 ga watan Satumba.

Advertisement

Shugaban kungiyar malaman makarantar Polytechnic (ASUP) na makarantar yace malaman basu goyi bayan haka ba kuma sun tabbatar ma dalibai cewa za'a cigaba da daukar darasi.

Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun soma yajin aiki don nuna adawar su ga tsarin biyan albashi mafi karanci da gwamnatin tarayya taki amincewa da zaman ta.

Kungiyar ta fara yajin aiki na wucin gadi wanda zai kai tsawon kwanan bakwai kai ga yadda yarjejeniya ta kasance da gwamnati.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement