Akwai jita-jita, cewa sanannen gidan abinicin Amurka mai suna “Kentucky fried chicken” (KFC), suna da niyar fita daga kasuwar nijeriya, farawa daga Jihar Lagos.
Wannan jita-jitan an fara a ƙarshen satin baya, akan Twitter, kuma yau, wasu shafin yanar gizo-gizo sun dauƙi wanna labarin.
KFC har yanzu ba su mayar da martani ga jita-jitan ba, amman akwai iƙirari wai, an fara rufe rassan su na jihar Lagos saboda ƙarancin ƙudin da suke samu kuma tsadar farashin sarrafa.
Ba duk rassan su za a rufe ba, in lallai labarin na gaskiya ne.
Duk da ɗaura wa koma bayan tattalin arziki laifi, an gan cewa, rashin gyara kausuwar su ne ya jawo wanna matsalar de suke fama.
Babban kamfani irin na KFC, abun mamki ne ace shafin kafofin watsa labari na twitter, facebook da instgram din su ba su aiki tun 2014. Sannan a yanzu ba su da shafin yanar gizo, duk waɗannan sun nuna cewa KFC su na da niyar barin kasuwar nijeriya, ko da ba a san hujjojin da ya sa ba.
Wani Gidan abinci mai suna, “Domino’s Pizza” sun buɗe rassa da yawa a jihar Lagos, a cikin wata 8, Dominos sun samu babban haɓakan arziki, su ma ba suna jin zafin koma bayan tattalin arzikin nijeriya ba? Kila samfurin kasuwancin su ya fi kyau.
KFC a 19 Disamba 2009 su ka buɗe rassan su na farko a city Mall, onikan, cikin jihar Lagos, a 2010 suka yi sanarwar niyar buɗe sabuwar rassa guda 20 a 2011.