Advertisement

Hukumar hana kauri ta kama bindigogi 1,100 kuma ta kama jami’an 2

Bindigogin sun shiga Nigeria daga ƙasar Turkiya
Advertisement

Hukumar hana ƙauri na kasa ta kama bindigogi 1,100 da aka shigo da su daga ƙasar Turkiya a shiyyar tashar jiragen ruwa na Tin can Island.

Advertisement

Kakakin hukumar Joseph Attah ya bayyanar da haka ranar litinin 11 ga watan Satumba.

“Mun kama bindigogi 1,100 da aka shigo dasu daga ƙasar Turkiya a tashar jiragen ruwa dake Legas. An fara bincike akan su kuma mun kama wani jami’in hukumar tare da wani magatakarda hukumar wadanda muke zargin cewa sun taimaka wajen shigowar bindigogin” inji kakakin.

Hukumar zata cigaba da bincike kuma zata gurfanar da wadanda aka kama gaban kotu.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement