Gwaman ya amince da kafa dokar kashe yan kungiyar asiri da aka kama a jihar sa
Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya sannu ga dokar hukuta duk wani dan kungiyar asiri ta hanyar kisa.
Matakin da gwamnan ya dauka ya nuna cewa gwamnatin sa ta shirya kawar da ayyukan ta'adanci a jihar Ekiti.
Gwamnan yace duk wani gini da ayyukan yan kungiyar asiri za'a kaddamar da ita ga gwamnati kuma za'a kulle duk wanda ke da ginin a gidan wakafi tsawon shekaru biyar ba tare da yin beli.
Shima kakakin gwamnan Idowu Adelusi ya kara haske akan batun inda yake cewa " Daga yau duk wanda ke cikin kungiyar asiri, imma yana rike da makami ko koma bayan haka indai an kama shi yana aikata laifi, hukunci shi kisa ne."
Tun ba yau ba al'ummar jihar ke fuskantar barazana daga yan kungiyar asiri musamman a makarantu.
A cikin watan octoba harin da wasu yan kungiyar asiri suka ga jam'iyar jihar inda aka suka kashe wasu dalibai guda biyu yayi sanadiyar matakin da gwamnatin jihar ta dauka.