Dino Melaye, wanda ke wakiltar kananan hukumomi bakwai ciki har da Lokaja na jihar,ya ketara bisa karanchi masu kada kuri'ar zaben kiranyen.
Hukumar zabe na kasa mai zaman kanta ta kaddamar da shirin zaben kiranyen ranar asabar 28 ga watan Afrilu bayan yunkurin da al'ummar mazabar sanata suka yi na yin haka.
Sai dai, kamar yadda hukumar INEC ta sanar, kashi 5 na masu kada kuria cikin 188,500 aka tantance kafin kuri'ar.
A sanarwar da ta fitar ranar lahadi a garin Lokaci, INEc ta sanar cewa sanatan yayi nasara ne bisa karancin yawan wadanda hukumar ta kayyade domin cigaban zaben.
Farfesa Ukente Morthy, wanda ya sanya hannu a takardar sakamakon zaben kuma ya sanar, ya ce sakamakon bai cimma ka'idojin da doka ta shata ba domin raba gardama.
Mutane 189,870 ne suka sanya hannu kan bukatar kiranye ga Dino Melaye daga cikin yawan mutanen yankinsa 351,416 da suka cancanci kada kuri'a.
Amma a cewar Farfesan adadin mutane 18,742 ne kawai hukumar INEC ta tantance a zaben Kiranyen.
Mai dan majalisar yace kan lamarin?
Dan majalisar wanda ke jinya a asibiti, sakamakon raunin da ya ji yayin da ya wuntsulo daga motar yan sanda, ya nuna farin cikin sa kan sakamakon zaben kiranyen kana yayi ma jama'ar da yake wakilta godiya bisa damar da suka bashi na cigaba da wakiltar su.
Yayi wannan ne, a wata sako da ya wallafa a shafin sa na kafar sada zumunta ta Twitter tare da jaddada cewa zai yi iya bakin kokarin sa wajen zama wakili na gari.
Sai dai kan batun kiranyen da ya faru, ana danganta sakamakon ga magudi ta hanyar yi ma shirin zagon kasa tare da saka sunayen matattu cikin sunayen wadanda suka goyi bayan kiranyen.