Advertisement

Rahama Sadau ta sake samun lambar yabo

Jarumar ta samu kyautar jaruma mai bada taimako wajen haddasa zaman lafiya  a bikin Peace Achievers Awards 2018 wanda aka gudanar ranar Asabar
Advertisement

Har yanzu tauraron fitacciyar jaruma Rahama Sadau na cigaba da haskawa inda ya samu wani sabon lambar yabo a karshen makon da ya shude.

Advertisement

Jarumar ta samu kyautar jaruma mai bada taimako wajen haddasa zaman lafiya  a bikin Peace Achievers Awards 2018 wanda aka gudanar ranar Asabar 22 ga watan Satumba a dakin taro na Transcorp hilton Hotel dake Abuja.

Rahama ta nuna farin cikin ta samun wannnan kyautar a shafin ta na kafafen sada zumunta.

Gasar Peace Achievers Awards biki ne wanda aka gudanar a ko wani shekara domin karrama fitattun hukumomi da yan kasar dake taka rawar gani wajen raya zaman lafiya a kasar.

Bikin gasar na bana shine karo na bakwai.

Advertisement

Kyautar da jarumar ta samu shine na uku da zata samu bana bayan na jaridar Leadership da gidauniyar Global Women Empowerment network.

Rahama Sadau ta sake fito takara a gasar Africa Movie Academy Awards na 2018 bisa rawar da ta taka a cikin shirin turanci mai taken "Hakun

Advertisement
Latest Videos
Advertisement