Shahararren dan luwadi na kasar Congo wanda aka fi sani da Paul Arnaud yayi mutuwa mai ban haushi bayan ya sha fama da ciwon daji na dubura.
A bisa rahoton da kafafen yada labarai da kasar suka fitar Arnaud ya rasu ne ranar 24 ga watan Octoba bayan ya kwashi wasu lokuta yana fama da ciwon.
Arnaud wanda ya shahara a fadin kasar ya kamu da cutar ne sandiyar barnar da yake yi da masoyin shi bature dan kasar waje.
Labari ya nuna cewa Arnaud wanda ya kasance dan dan limamin coci ne ya kaurece iyalinsa bayan sun nuna rashin alaka dashi yayin da suka gano cewa yana luwadi.
Arnaud ya canja sheka daga ainihin garin shi zuwa babban birnin kasar Congo inda ya samu damar cigaba da fasikancin da yake yi.
Bayan wasu yan shekaru ya gamu da ciwon wanda ya sha fama da jinya na kusan shekara bakwai amma bai kai ga samun lafiya har ya mutu.