Advertisement

Sanannen mai garkuwa da mutane ya shiga hannun hukuma

An kama shi yayin da yake jima'i da budurwar sa a maboyar sa dake jihar Bayelsa
Advertisement

Gawurtaccen mai garkuwa da mutane Godwin Alamingo wanda jami'an tsaro suka dade suna neman shi ruwa a jallo ya shiga hannun hukuma.

Advertisement

Rundunar yan sanda na reshin jihar Bayelsa sun kama shine yayin da yake jima'i da budurwar sa a maboyar sa dake nan jihar.

Bisa rahoton da News-times ta fitar Daddy Abuja ya fice wajen yin fashi a jihar Delta, Bayelsa, Imo da Rivers da dai sauran jihohin yankin kudancin Nijeriya.

Yayi garkuwa da mutane da dama cikin har da kanwar gwamnan jihar Bayelsa mai suna Nancy tare da wani attajirin dan kasuwa mai suna Amaebi Afere.

Jami'an tsaron sun shaida cewa basira da kuma bin diddigi cikin tsari suka kama shi.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement