Advertisement

Arsene Wenger, kociyar kungiyar Arsenal yayi murabus

Zai bar kungiyar ne a karshen kakar bana kamar yadda ya sanar a wata takarda da ya fitar ma kungiyar
Advertisement

Kociyar ya kwashi tsawon shekaru 22  yana horas da sannanen kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila.

Advertisement

Zai bar kungiyar ne a karshen kakar bana kamar yadda ya sanar a wata takarda da ya fitar ma kungiyar.

Kamar yadda labarin ya fito a shafin kungiyar ta yanar gizo, Arsene Wenger yana ma kungiyar da dinbim magoya bayan ta dake ko'ina a fadin duniya godiya game da damar da aka bashi na jagorantar tawagar yan wasan ta na tsawon shekaru 22.

Dan kasar faransa mai shekaru 63, shine kociya mafi dadewa a tamaular firimiya na Ingila kuma yayi nasarar horar da Arsenal a wassanni 823.

Yayi murabus ne kafin karewar kwantiragin sa wanda sai cikin kakar badi zai kawo karshe.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement