Laolu Akande, mataimakin kafofin watsa labaru, ya bayyana cewa tawagar Shugaba Buhari da mataimakin sa, Farfesa Osibanjo mai karfi ne.
A cikin tattaunawa tare da pulse, ya ce shugaban ƙasa Buhari da mataimakin sa farfesa Osibanjo na da buri iri guda.
“Zumuncin dake tsakanin su mai inganci ne” ya ce.
“Abun da ku ka gani, shi ke faruwa a ɓoye , akwai mutunci tsakanin su”
“Mataimakin Shugaban ƙasa ya faɗa min cewa shugaban ƙasa na wahayi zuwa gareshi. sadaukarwar shi ga talakawan nijeriya, sadaukarwar shi ga yin ayyuka masu kyau, duk sun zama abun wahayi gare shi, tun kafin ya zaɓe shi ya zamo mataimakin sa.
Shugaban ƙasa, ba biɗar tabattar da komai yake yi ba, ba kuɗi ya ke yi biɗa ba, ba ɗan kasuwa bane, bai taɓa kasuwanci ba, mataimakin shugaban ƙasa Osibanjo mutum mai halayya na ƙwarai ne, tare da shugaban ƙasa” ya ce.
Ya buƙaci yan Nijeriya su ƙara haƙuri game da gwamnatin shi, wai zai cika alƙawalin shi.