Lai Mohammed ya ce Shugaba ba shi da wani rashin lafiya
Ministan bayanai Lai Mohammed ya sallame rahotani cewa, Shugaba Muhammadu Buhari bai da lafiya.
Sabuwar shati faɗi game da lafiyar Buhari ta taso a ranar Laraba, Afrilu 12, bayan bai zo taron Federal Executive Council (FEC) na sati ba.
Mohammed ya faɗa wa ƴan gidan wakilan jihar a ƙarshen taron wai lafiyar Shugaba ƙalau.
Ya ƙara cewa shugaban ƙasa na ɗauke da ayyukan sauran jihohi a lokacin taron FEC.
Mataimakin shugaban ƙasar, Yemi Osinbajo shi ya shugabantar da taron.
Shugaban ƙasa bai sake rashin lafiya ba, Shugaban ƙasa na a gari. Shugaban ƙasa na halarta wasu lamari. Ya duba ajanda na taron, kuma ya yanke shawarar cewa mataimakin shugaban ƙasa ya jagoranta taron. ba sabon abu bane mataimakin shugaban ƙasa ya jagoranta taron FEC ba" Mohammed ya ce.
Wannan shi ne farko da Buhari zai yi rashin kasancewa a taron FEC, tun lokacin da ya dawo Nijeriya, bayan kwana 49 da ya ɗauka hutun duba lafiyarsa a london.
A kan isowa a Najeriya, Buhari ya ce, bai tuna da taba yin irin wanan rashin lafiya ba a duk rayuwarsa.
Ya kuma ce zai cigaba da neman hanyar jinya lafiyar sa.
A halin yanzu ,shugabanci ta bayyana cewa, Buhari zai samu ƙarin magani a London ba a Najeriya ba.
A ranar Alhamis, Maris 30 ,Kakakin Buhari, Garba Shehu ya ƙaryata rahotanni wa Buhari zai kawo likitocin sa zuwa Najeriya.