Rahotanni sun nuna cewa sojojin saman Nijeriya sun kashe matar shugaban kungiyar boko haram Malama Firdausi a yankin Durwuwa dake wajen garin Urga nan Konduga.
Wannan labari a fito a wata sanarwa wanda rundunar sojojin sama ta bayyana wa manema labarai kuma mai magana da yawun rundunar Air Commodore Olatokunbo Adesanya ya sanyawa hannu ranar laraba a 25 ga wata a garin Abuja.
Rundunar tace rahotanni sun nuna cewa malama Firdausi taje wakiltar mijinta ne a wata taro da sauran mayakan kungiyar inda sojojin suka kai harin saman.
Rahoton da aka tattara ya nuna cewa harin saman da aka kai ya sa wuta da tashi wanda ya lalata ginin da mayakan suke ciki har wasun su suka mutu ya kuma sanya wasu daga cikin su sun tsere.
Dama a baya rundunar ta sanar cewa zata fara kai hare-haren sama ga mayakan boko haram a wata aiki wanda tayi wa lakabi "operation ruwan wuta".
Har ila yau Shekau bai shiga hannu ba tunda kungiyar da fara fafutikar ta'adanci a arewacin kasar a 2009.