Advertisement
Tsohon gwamnan jihar Sakkwato ya sanar da hakan ne yayin da ya gana da manema labarai a garin Bauchi ranar Lahadi 23 ga wata.
Advertisement
Daya daga cikin yan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jamiyar PDP, Attahiru Bafarawa yace zasu goyi bayan duk wanim dan takara da yayi nasarar zama gwanin jamiyar gabanin zaben 2019.
Advertisement
Bafarawa yace ba matsala bane ganin cewa cikin yan takarar zama gwanin jam'iya akwai gwamnan jihar sa, Aminu Waziri Tambuwal, domin sun sha alwashin mara ma duk wanda yayi nasara baya a zaben.
Yace babban burin su shine su kwato kujerar mulkin kasa daga jam'iyar mai mulki ta APC.
Tsohon gwaman ya kara da cewa bai shigo siyasa don neman kudi, yace ya shigo ne domin yayi wa al'umma aiki kuma yana ganin shi yafi cancanta domin yana kwarewa a harkar siyasa duba da shekaru takwas da yayi a matsayin gwamnan Sakkwato.
Advertisement
Subscribe
Sportal WhatsApp
Latest Videos
Nigeria hausa
Gobara tayi sanad in mutuwar mutum 35
11.09.2018
Advertisement
Videos
Advertisement
Advertisement