Advertisement

Classiq ya raya ranar haihuwar shi da sabon Album

___8884927___2018___9___21___13___classiq_39902799_541532416316853_1751958367944283600_n
___8884927___2018___9___21___13___classiq_39902799_541532416316853_1751958367944283600_n
Domin raya wannan rana mai muhimmi a rayuwar shi, mawakin zai fitar da faifan sabbin wakokin shi domin nishadin masoyan sa da masu bibiyan wakokin sa.
Advertisement

Hazikin mawakin hausa hip-hop Barnabas Buba Luka wanda aka fi sani da Classiq ko Captain sama yana murnar zagayowar ranar haihuwar sa yau 21 ga watan Satumba.

Advertisement

Kamar yadda ya sanar a shafin sa na Instagram mawakin wanda aka yi ma lakabi da 'Arewa mafia' zai kaddamar da wakokin ne a wajen taron biki da aka shirya masa musamman domin murnar ranar haihuwa.

___8884929___2018___9___21___13___classiq_40825487_672280803144044_850666205555109204_n

Sabon faifan wakokin shine "The New North" kuma wakoki Takwas ne a cikin ta.

Wasu daga cikin mawaka da ya saka a cikin ta sun hada da Ice Prince Zamani, Ckay da Yung L.

Advertisement

Kasancewa yau take ranar haihuwar shi ne ga wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da shi ;

1. Dan jihar bauchi

Wannan mawakin da aka haifa ranar 21 ga watan Satumba na 1991 haifaffen dan jihar Bauchi ne kuma shine da na karshi cikin yara 3 da iyayen sa suka haifa.

___7351458___2017___9___21___13___20688403_107670493277257_1225398016869924864_n

2. Baban shi malami ne

Advertisement

Kwarrai ko kana iya kiran shi da “dan mallam” domin shima na alfahari da haka kasancewa babban shi malami ne a jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake nan jihar Bauchi. Baban shi likita ne na boko a fannin ilimin “geography” ita kuma uwar sa malama ce a asibiti.

___7351466___2017___9___21___13___19765212_1216344368488413_3471186448298803200_n

3. Yayi karatun sa a Arewa

Shidai wannan jarumin waka ya fara karatun sa na firimari garin Bauchi kuma ya kammala karatun digiri dinsa a jami’ar Ado Bayero dake Kano inda yaa karanta ilimin kwamfuta.

Classiq tare da Sani Danja
Classiq tare da Sani Danja
Advertisement

4. Ya yayi wasa a garuruwa da dama kuma jakadan arewa ne

Classiq ko kuma “arewa Mafia” kamar yadda yake ma kansa lakabi yayi wasa a wurare da dama kuma ya yi waka tare shahararrun mawakan Nijeriya.

___7351513___2017___9___21___14___18513104_1723735507918995_4589735024693084160_n

5. Duk wakar shi akwai dangantaka da Arewa

Ko cikin baitutukar shi ko sunnan wakar ko kuma yanayin shigar shi a bidiyo zai ka ji ko ka gan abun da ya ganganci arewa. Duk da cewa wannan mawakin yana iya basaja ya koma wakokin turanci amma ya amince da ya dabbaka yaren ga idon duniya.

Advertisement
___7351551___2017___9___21___14___18298907_1787535811561565_6512574252271534080_n

yayi wakoki irin su Zauna, Sama, hoto, barka da sallah, Ana haka da dai sauransu.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement