Advertisement

Mutum huɗu a kotu bisa zargin sace shanu 6

Cow
Cow
Wanda ya gurfanad da su a kotu, Sgt. Adam Owochio ya faɗa wa kotun cewa a Maris 31, ƙungiyar ƴan sanda sun tsare mutanen, a ƙarƙashin jagorancin Insp. Philip Lorpuu.
Advertisement

A ranar Laraba An gurfana Mutum hudu a gaban Kotu  da zargin su da sace shanu shida.

Advertisement

Mutanen da aka tuhuma a kotu: Linus Yachiga,John Tsege, Oota James da Abdullahi Umaru, basu amsa laifi ba akan zargin ƙirga-biyu na laifin haɗin kai da kuma sata.

Wanda ya gurfanad da su a kotu, Sgt. Adam Owochio, ya faɗa wa kotun cewa a Maris 31, ƙungiyar ƴan sanda sun tsare mutanen , a ƙarƙashin jagorancin Insp. Philip Lorpuu, na ofishin ƴan sanda ta Adikpo.

Ƴan sandan sun tsayar da babbar mota a kan Jato-aka, titin Gboko, mai Reg lamba ENU-449-ZX, ɗauke da shanu shida, mai yiwuwa an sato.

Owochio ya ce, a lokacin da aka tambaye waɗanda ake zargi, yadda suka samo shanun, suka kasa bada amsa mai gamsarwa.

Advertisement

Ya ce binciken lamarin har yanzu na tafiye, sannan ya roƙi kotun domin a ɗage sauraren.

Ya ce laifukan su saɓa wa Sashi na 97 da 321 na dokokin Jihar Benue na 2004.

Alƙalin Kotun Majistare, Mrs Franca Yuwa, ta bayar da belin N50,000, kuma kowane da mai ɗaukar nauyin sa.

Ta ɗaga lamarin zuwa May.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement