Advertisement

Yan IPOB sun kashe wani jami’in dan sanda

An kai harin sakamakon hartabo da sojoji suka yi da wasu daga cikin mabiyan ƙungiyar a jihar Abia
Advertisement

Wasu daga cikin yan Kungiyar faffutikar kafa ƙasar biyafara (IPOB) sun kashe wani jami’in dan sanda a titin Oyigbo dake garin Port harcourt na jihar Ribas.

Advertisement

Kwamishnan yan sanda na jihar Zaki Ahmed ya tabbatar da harin wanda yayi sanadiyar kashe jami’i daya tare da jikkata jami’in biyu  ranar laraba 13 ga watan Satumba.

Bisa ga rahoton da Thecable ta ruwaito harin da yan ƙungiyar suka kai wa jami’an yan sanda ya faru ne sakamakon hartabo da sojoji suka yi da wasu daga cikin mabiyan ƙungiyar a jihar Abia.

Kwamishnan ya sanar cewa wannan shine karo na biyu da yan IPOB zasu kai hari ga yan sanda a jihar.

Ya kara da cewa mabiyan IPOB sun kona motar sintiri da jami’an kuma sun kwace alburushi daga hannun jami’in da suka kashe.

Advertisement

Zaki Ahmed yace hukumar yan sanda na jihar ta dauki mataki na kawar da bazuwar ire-iren farmaki da mabiyan IPOB keyi kuma zata iya bakin kokarin wajen hukunta duk wanda ke da hannu a harin.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement