Pulse.ng logo
Go

Yaki da ta'adanci Sojoji sun kama jigo a kungiyar Boko haram

Sojojin sun kama dan ta'addar a wata sansanin yan gudun hijira dake nan Banki a jihar Borno.

  • Published:
Sojoji sun kai farmaki ma wadanda suka kai hari ga al'ummar Ancha (daga premium times) play

Sojoji sun kai farmaki ma wadanda suka kai hari ga al'ummar Ancha (daga premium times)


Join the "sabi" clique. Don't miss a thing, get the latest updates to fuel your conversation daily

By signing up , you agree to our Privacy Policy and European users agree to the data transfer policyThank You! You have successfully subscribed to receive pulse.ng daily newsletter.

Dakarun sojojin Nijeriya sun kama wani jigo a kungiyar yan ta'adar boko haram wanda suka dade suna neman shi ruwa a jallo tare da sauran masu ruwa da tsaki ma kungiyar.

Rundunar tace ta kama dan kungiyar, Maje Lawan a wata sansanin yan gudun hijira dake nan Banki na jihar Borno. Mutumin da aka kama shine lamba 95 cikin jerin sunayen mayakan boko haram 100 da sojojin ke nema ido-rufe.

Labarin haka ya fito ne a cikin wata takarda da kakakin rundunar Birgediya janar Texas Chukwu ya sa hannu kana aka fitar wa jama'a.

A cikin sanarwan, kakakin yace kawo yanzu yana hannun sojojin inda suke cigaba da bincike kan lamarin gabanin mika shi ga hukumar da ya dace.

Kakakin ya kara da cewa dakarun sun kuma dakile harin kunar bakin wake da wasu yan ta'ada suka kai garin Malari sakamakon shirin kwantar bauna da suka yi masu.

Yace an gani kekuna 10 tare da yan ta'addar.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement