ADVERTISEMENT

Sakacin jami'an tsaro yayi silar sace yan matan Dapchi - inji amnesty International

Kungiyar tace sai da aka sanar ma jami'an tsaro shirin da boko keyi gabanin harin amma sun musanta labarin

Sakamakon harin da mayakan boko haram suka kai a ranar 19 ga watan febreru, yan ta'adar sun sace yan matan makarantar gwamnati na kimiya da fasaha dake nan garin Dapchi su 110.

A bisa bayanin kungiyar, sai da aka sanar da jami'an tsaro sa'o'i hudu kafin mayakan su kai harin amma jami'an sojoji da yan sanda basu dauki wata mataki na bayar da kariya kan lamarin.

Amnesty ta kara da cewa yawancin shugabannin al'umar yankin, sun sanar da sojoji tun lokacin da suka samu labarin jerin gwanon motocin maharan na wani kauye mai nisan kilomita 30 daga garin na Dapchi, kwana guda gabannin sace 'yan matan.

Duk da zargin da kungiyar tayi kan jami'an tsaro na yin watsi da labarin da aka sanar masu sa'o'i hudu gabanin isowar yan ta'adar, wani jami'in dakarun sojoji ya karyata labarin yayin da ya zanta da jaridar Reuters.

ADVERTISEMENT

Jagoran kungiyar na Nijeriya Osai Ojigho ya bukaci gwamnati da tayi bincike kan lamari.

Matakin gwamnati tarayya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar ma iyayen daliban cewa gwamnatin sa zata iya bakin kokarin ta wajen kubutar da yaran yayin da ya kai ziyarar jaje ga iyayen.

Shugaban yana mai cewa "Babu hutu har sai baya an samu nasarar kubutar da yaran da aka sace".

Hakazalika, a jawabin sa yayin da ya amshi bakoncin tsohon sakataren ayyukan waje na Amurka, shugaban ya bayyana cewa a shirye suke wajen neman sulhu da Boko haram domin kubutar da yan matan.

ADVERTISEMENT

Sace yan matan  ya biyo shekara hudu bayan faruwar kwatankwacin haka a garin Chibok inda yan ta'ada suka kai hari makaranta government girls secondary har suka yi nasarar sace yan matan makarantar su 276. Bayan sasantawa da kungiyar, an yi nasarar kubutar da wasu daga cikin yan matan. Sama da yan mata 100 ke hannun yan ta'addar har yanzu.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

Recommended articles

Bella Shmurda seemingly throws shade at Naira Marley in new tweet

Bella Shmurda seemingly throws shade at Naira Marley in new tweet

Africa is set to welcome the idea of borderless trade within the continent

Africa is set to welcome the idea of borderless trade within the continent

'For commodification of the naira, use cassava' [Pulse Explainer]

'For commodification of the naira, use cassava' [Pulse Explainer]

5 outfits for 5 days of work inspired by Regina Daniels

5 outfits for 5 days of work inspired by Regina Daniels

African countries by Netflix' contribution to their GDP

African countries by Netflix' contribution to their GDP

Sleep paralysis: Caused by witches or a natural occurrence?

Sleep paralysis: Caused by witches or a natural occurrence?

Mohbad records 6 entries in top 10 of TurnTable Top 100

Mohbad records 6 entries in top 10 of TurnTable Top 100

5 things women put on that men find instantly attractive

5 things women put on that men find instantly attractive

I will be returning to assist with the investigations - Naira Marley

I will be returning to assist with the investigations - Naira Marley

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT