Dan majalisa yayi karin bayani kan yadda yayi sa'o'i 11 a saman bishiya yayin da yan bindiga suka kai masa hari
Dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar jihar Kogi ta yamma Dino Melaye ya bayyana yadda yayi saoi 11 a kololuwar saman bishiya don kauce ma yan bindiga da suka kai masa hari hanyar shi na zuwa johar sa domin halarta zaman kotu.
A makon danya gabata ne muka samu labari cewa wasu da ake zargin cewa yan bindiga ne suka kai ma motar dan majalisar hari a daidai unguwar gwagwalada.
Bayan kwana daya da faruwar haka sanatan ya bayyana kansa tare da sanar cewa ya nemi mafaka tsibirin daji domin neman mafaka.
Ya kuma yi ma Allah godiya bisa nasarar da ya samu na kubuta daga hannun yan bindigar. Yayi hakan ne a shafin sa na Twitter tare da yi ma jama'a godiya bisa addu'o'in da suke masa da kuma kulawar da suka nuna masa.
Yadda ya kaurace ma yan bindiga
Hirar shi da jaridar Premium times, Sanata Dino Melaye yayi karin haske game da halin da ya shiga.
Kamar yadda ya kara, yan bindigar basu dukufa ba domin sai da suka dauki shawarar kone motar shi. A cikin kokarin da suke da yin haka ya samu damar guduwa zuwa cilkin daji.
Dino Meyale yace yayi nasarar kaurace masu duk da cewa sun biyo shi da gudu cikin dajin. Yace ya haura saman bishiya kuma nan ne ya nemi mafaka har sai da yan bindigar suka yi saduda har suka koma.
Dan majalisar yace yana sa ran motocin da suka kai farmaki ga motar sa daga rundunar yan sanda ne domin ya ya gane su tun zaman kotu da ake yi a kan karar da aka shigar a kansa ranar ranar laraba 25 ga watan Yuli.
Yace bai iya gane fuskokin wadanda suka kai masa hari domi a lokacin da lamarin ya faru hankalin shi tana kan yadda zai tsira da rayuwar sa.
Kaurace ma zaman kotu
Ya kuma yi watsi da rade-raden dake yawo na cewa ya shirya wannan ne domin kaurace ma zaman kotu da aka shirya kan karar da aka shigar a akan sa.
Dan majalisar bai samu damar hakartar zaman kotu da aka shirya ranar Alhamis 26 ga wata sakamakon abun da ya faru.
Yana fuskantar tuhuma ne kan zargin laifufuka da suka dangancin sata da goyon bayan barayi.
Bayan bayani da wakilin sa yayi ma kotu kan, babban alkalin kotun Sullyman Abdullah ya daga ranar cigaba da zama kan karar zuwa ranar 9 ga watan Agusta.