Advertisement

Yan bindiga sunyi awon gaba da dan majalisar dattawa mai wakiltar jihar Kogi

Sanata Ben Bruce ya sanar da hakan inda yace yan bindigar sun tare motar Dino Melaye a daidai unguwar gwagwalada hanyar sa zuwa jihar Kogi domin halartar zaman kotu a jihar Kogi kan tuhumar da ake masa.
Advertisement

Labari mara dadi ya fito daga birnin tarayya mai bayyana cewa wasu da ake zargin cewa masu gurkuwa da mutane ne suka sace dan majalisar dattawa sanata Dino Melaye.

Advertisement

Kamar yadda takwaranshi na majalisar Sanata Ben Muray Bruce ya sanar a shafin sa na twitter, anyi awon gaba da sanatan a daidai unguwar gwagwalada hanyar sa zuwa jihar Kogi don gabatar da kanshi gaban kotu kan tuhumar da ake masa.

Sanata Ben Bruce ya sanar cewa ya samu wannan labarin ne a daga dan uwan Dino Melaye.

Sauran bayani zai fito nan gaba.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement