ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Sana'ar waka da koma bayan da mawakan arewa ke fuskanta

Shahararren mawakin yace babban abun da ya jawo haka shine "Mu yan arewa mune matsalar. Muna lacking support daga mutanen mu. duk inda ka gan industry babban abun dake sa su cigaba shine al'ummar su ne."

kai ga yanzu babbu wani mawakin hausa ko arewa da ya samu karbuwa har tauraron sa ya kai sassa daban daban dake fadin kasar ko sauran kasashen duniya.

Kai zaka ce ganin yadda yaren hausa ta kasance daya daga cikin harsunan da ta shahara a nahiyar Afrika hakan zata taimaka wajen daukaka masu yaren.

Idan aka duba akalla mutane 150 ke magana da yaren Hausa amma hakan bata taimaka wajen cinma burin mawakan dake fitar da fasahar su cikin yaren. Shin ko mai ya jawo hakan?

ADVERTISEMENT

Shin akwai lokutan da zuciyar mu take cike da kunci game da yadda wakokin hausa da mawaka dake fitar da fasahar su da harshen hausa ke fuskantar barazana na rashin yaduwa zuwa sassa daban-daban dake fadin Nijeriya har ma da sauran kasashen duniya?

Wasu lokaci na kan yi tunani ko dai wakokin akwai sinadarurraka da ta rasa wanda don shine bata samun karbuwan da ya kamata?. Sai dai sau da dama wannan tunanin tawa ta sha zagon kasa domin kuwa waka da arewa tamkar jummai ne da dan jummai kuma dangantakar su ya fara tun iyaye da kakanni.

Wajen watsa ma tunani na ruwan tsanyi sai na tuna da irin gudunmawar da fitattun jaruman arewa da suka kafa tarihin tare da kafa tambarin alama a farfajiyar nishadi na kasa sai zuciya ta ta samu sukuni.

Rawar da iyaye kamar su Mamman Shata, Dankwairo, Bala mila, Dan maraya jos,Haruna uji, barmani Choge da sauran su suka taka kai ga yanzu bata gama gushewa ba a zukata.

Wani daga cikin iyayen mu da suke raye a lokacin da wadannan jarumai ke cin keren su babbu babbaka yace a  zamanin su "Idan daya daga cikin wadanan basu yi wasa a taro, gaskiya taro bai kai taro ba".

ADVERTISEMENT

Dattijon wanda ya nemi a sirrance sunan sa yace shi dai a iya sanin sa mawakan arewa da suka taka rawar gani sun hada da Adamu Danma, Naranbada, Ahmadu Doka, Dankwairo, Auta Dabai, Maman Sarkin Taushin Katsina, Ali Dan Turaki, Haruna Oji, Garba Super, Dan ba'u.

A bangaren mata kuma yace akwai, Uwani Zakirai, Uwaliya mai Amada da Barmani Choge.

Yace sun nishadantar da al'umma matuka kuma tauraron su ya haska har zuwa sauran kasashen duniya.

A bisa bayanin sa Mamman shata da Dan maraya Jos sun fi samun daukaka domin kuwa a kasar Ingila sun tafi don yin wasa.

Ta'asirin basirar su yayi yawo lungu da tsako a arewa da ma sauran jihohin kasar.

ADVERTISEMENT

Domin samun amsar tamboyi na na tuntubi wasu fitattun mawaka dake cin gashin fasahar a zamanin nan.

Mai ya haifar da wannan koma-bayan

Ban ida furta tambayar ba Ali jita ya katse anzari na, kamar dama abun ya daure masa kai.

Dalilin da yasa ya fadi haka shine " Ba ma alfahari da mawakan mu" . Yace abu mai sauki ne ka gan wakokin mawakan kudancin kasar yayi tasiri a garuruwan dake  jihohin arewa amma abun takaici wakokin yan asalin baya taka kara ya karya a nan balle ya tsallake zuwa sauran sassa.

Ya cigaba da cewa "Goyon baya ma'an da kudin su da duk wani abu da suke bukata zasu yi masu. Sa'anan in suka tashi yin abun zasu zo kalle su kuma suyi alfahari dasu da abun da suke yi tunda suna wakiltar su ne. Wanda shi kuma a arewacin Nijeriya musamman mu nan irin su bakano da sauran su ba haka bane. yawanci ma akwai kyama in kana abun ana gani da raini ana ganin kai ba komai bane. Za'a iya cewa hassada ce ko wasu kyashi ne. wasu kuma rashin fahimta ne tunda an fahimci waka da harkar wasan kwaikwayo tun a da cewa wasu kaskantattun mutane ke yin ta, wanda kuma ba haka bane."

ADVERTISEMENT

Yace idan aka duba sauran yaruruka akwai hadin kai kuma suna taimakon mawakan su amma akasarin haka ke faruwa a arewa.

Maganar tashi sai ta tuna mun da fashin baki da wani matashin mawaki yayi mun yayin da na zanta dashi.

Abu na biyu na daga cikin abubuwa da ya haifar da komawa bayan harkar kamar yadda ya kara shine rashin ilimin sana'ar daga wasu mawakan. Yace "yawanci an shigo abun da ka" kuma wasu sun shigo ne bisa rashin abun yi bayyan kammala karatu ba tare da sanin abubuwan da ta kunsa.

Maganar tashi sai ta tuna mun da fashin baki da wani matashin mawaki yayi mun yayin da na zanta dashi.

Mawaki hausa-hip-hop, Lyrical Dr Smith, ya nuna takaicin sa yadda idan an shirya wasa a Arewa kuma aka gayyaci mawaka dake zama a legas sai a biya su da kudin alakoro amma bakin kuwa sai dai su Koma da farin ciki bisa yawan yawan kudi da suka samu a wasan wanda yan arewan suka girgaza taro tare da birge jama'a.

ADVERTISEMENT

Kalaman matashin mawakin ya tabbatar mun da cewa akwai mawaka masu tarin basira da fasahar waka a arewa sai dai amma basu samu cibiya wanda zai daukaka basirar su.

Shima shahararren mawakin gambara wato rap, Terry tha Rapman, wanda yayi fice a kudancin kasar kuma yana daya daga cikin jagororin wannan fannin waka a kasar yayi tsokaci game da hakan.

Yana mai cewa "A farko dai idan kai mawakin arewa ne mawuaci ne ka samu daukaka a kudu musamman idan baka da manya da zasu mara maka baya."

Dan asalin jihar Nasarawa ya kara da cewa  a wani bangare kuma matakai na al'ada da addani yana daga cikin abubuwa da ya haifar da rashin cigaba ga mawakan arewa. Yace wasu sunyi na waka mummunar fahimta.

Matakin da za'a dauka

ADVERTISEMENT

Na tambayi mawakan Kan wani irin mataki ya kamata a dauka domin farfado da harkar waka a arewa har su samu su kai inda ya kamata, ga amsar da suka Bani kamar haka:

Ali jita yace ya kamata yan kasuwa su sa hannu wajen zuba jari a masana'antar kasancewa zamani ya can duba da yadda waka ta samu karbuwa a duniya kuma tana daya daga cikin abubuwan dake bunkasa kasuwanci.

Ya kara da cewa akwai kuma bukatar wayar da kan al'umma wajen sanin amfanin yin waka da abubuwan da ta kunsa da irin ta'asiri da take haifa a cikin al'umma.

Hakazalika mawakin wanda ya shafi sama da shekaru 10 yana sana'ar yace lokaci yayi da yan kasuwa zasu zuba jari a fannoni daban tare da yin amfani da yadda zamani ke tafiya wajen cin moriyar kasuwancin su.

Daha karshe yayi kira ga gwamnatiu

ADVERTISEMENT

Ita ma Mawakiyar kamfanin Mavin Records Hadiza Blell wanda aka fi sani da Di’ja tana da ra’ayin cewa matukar ana neman cigaba dole a fara daga gida.

Tace “A duk halin da ka tsinci kanka sai ka gode masa. Akwai artist da suka suna a nan Legas amma asali daga arewa aka far jin su. Ina gani idan aka fara daga gida zai taimaka.”

A bangaren sa, Terry tha Rapman, yace shi ya zage damtse kuma ya daure dammara domin kawo gyara tare da bada goyon baya sa ga dinbim matasa masu sha'awar yin waka domin bayyana fasahar su.

Yace daya daga cikin abubuwan da mawaka zasu yi shine su dage wajen fitar da wakoki mai ma'ana kuma wanda zai kayyatar da jama'ar arewa. Ya Kara da cewa idan har mawakan sun tabbatar da sun fitar da kayyatatu wakoki toh su dage wajen fitar dashi ga kunnuwan jama'a ta hanyar gidajen rediyo da telibijin da makamantar su. Yace yin haka yana daga cikin abubuwan da yasa ake jin wakokin sauran mawaka wadanda ba yan asalin yanki ba da kuma sauran mawakan kasashen waje.

Yace shima yana shirya wani kunshin wakokin wanda zata kunshi labarin yan arewa da al’adar ta.

ADVERTISEMENT

Haifafen dan garin jos yace zai Koma arewa don fitar da labarin mutanen sa ba wai ya zauna a legas da tunanin yana magana da muryar Yan arewa alhali bai ziyarci yankin ba.

Gabanin gama tattaunawar mu, jarumin ya ba mawakan arewa shawara a kan su yawaita yin aiki da sauran abokan sana'ar su domin kuwa tana  taimakawa matukar wajen haska tauraro. Ya bada misali da ayyukan da fitattun mawaka, Classiq da Morell suka yi Wanda ya kara sa mutane suka tarbe su da hannu biyu.

Hausa suka ce da mugun rawa gare kin tashi, don haka masu fasaha da basirar yin waka tuta ya dawo gare ku gareku lokaci yayi da wakokin ku zai mamaye gidaje da wuraren nishadi.

Daya daga cikin shawara da na samu daga shahararren dan kasuwar harkar waka a cibiyar nishadi ta nahiyar Afrika, Bizzle Osikoya shine “matukar mawakan arewa na son su cinma manufar su a waka toh ya zama lalle su fara daga gida. Kada su sa a ran su cewa sai sun taho jihar Legas zasu samu daukaka.”

Da wannan dai na ajiye alkalami na da fatan nan gaba wakokin yan arewa zai mamaye kasar da sauran kasashen duniya.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT