ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya ya rasu

Tsohon ministan kudi kuma jigo na jam'iyar PDP ya rasu yana da shekaru 84 a duniya

Kamar yadda jaridar Daily trust ta ruwaito, marigayin ya rasu a wata asibitin kudi dake garin Abuja bayan wata rashin lafiya da ya sha fama da ita.

Tsohon jigon jam'iyar PDP ya rasu ranar alhamis 4 ga watan Yuli kuma yana yana da shekaru 84.

Haifafen dan garin Potiskum dake jihar Yobe, shine gwamnan babban banki tsakanin watan Satumba na 1975 zuwa Yuni na 1977.

ADVERTISEMENT

Bayan haka ya rike matsaayin ministan kudi karkashin mulkin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, wa'adi na farko na mulkin sa.

Bugu da kari shine shugaban yakin neman zabe na Obasanjo yayin da tsohon shugaban ke neman zarcewa a zaben 2003.

Gabanin rasuwar sa, marigayin ya taka rawar gani a harkar siyasar kasar.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT