ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Ga wasu abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da 'limamin mata'

Mun kawo maku wasu abubuwa biyar da muke son ku gane dangane da hazikin jarumin fim kuma mawaki.

___8875834___2018___9___19___16___adogwanja_33404986_2090561734491364_4668304789879128064_n

Jarumin wanda tauraron sa na cigaba da haskawa a fagen nishadantarwa ya samu karbuwa a zukatan masoya masu bibiyan fina-finan hausa.

Hakazalika yana da farin jini a fagen waka musamman daga mata duba da irin wakokin biki da yake rairawa. Bisa ga wannan dalilin aka yi masa lakabi da 'limamin Mata'.

ADVERTISEMENT

Mawakin yana daya daga cikin fitattun yayyan kamfanin White house Family wanda Adam A.Zango ke jagoranta.

Sanin kowa ne cewa Zango maigidan sa ne hakazalika shima mawakin baya boye ma jama'a dangatakar dake  tsakanin su.

Mun kawo maku wasu abubuwa biyar da muke son ku gane dangane da jarumin kamar haka;

1. Shi ruwa biyu ne

Duk da cewa shi dan asalin jihar Kano ne, Mahaifin sa dan garin Warawa ne dake Kano kuma mahaifiyar sa yar kabilar shuwa Arab ce daga jihar Borno.

ADVERTISEMENT

2. Karatun sa

Ado Gwanja yayi karatun firamaren sa a makarantar Babbangiji dake Karkasara. Sannan yayi karatun sakandare a Sakandiren kofar Nasarawa.

Bai samu ya cigaba da karatun sa bayan bayan Sakandare. Bayan rasuwar mahaifin sa jarumin ya shiga buga-bugar rayuwa har Allah Ya kawo shi zuwa ga matsayin da yake yanzu.

3. Harkar waka ya fara

ADVERTISEMENT

Yawanci ana ganin cewa jarumin ya fara da harkar sai dai a yanda ya bayyana, ya fara aiki a masana'antar nishadi ta fagen waka. Yace sama da shekaru 12 yake waka sai dai kuma a wancan lokacin ba'asan shi kana bai samu kudin shiga situduyo ba don buga waka.

4. Wanene gwanin sa

Hakika dangantakar shi da sauran mawaka mai kyau ce kuma akwai girmamawa tsakanin, mawakin yace babban gwanin sa a wannan harkar shine mawaki Aminu Maidawayya.

ADVERTISEMENT

5. Dalilin da yasa ya fiye yin wakar mata

Sanin kowa ne cewa hazikin mawakin ya fiye yin wakokin biki wanda ana iya cewa wakokin mata ne sai dai mafi yawanci ba'a san dalilin da yasa ya shahara a wannan fagen ba wanda yasa ma har ake kiran sa da 'limamin mata'.

A cewar shi dalilin da yasa yake yin wakokin mata shine domin mata sune iyayen biki kuma masu iya magana sukan ce  inda baki ya karkata ta nan yawu kan zuba.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT