A ranar Laraba, 9 Nuwamba 2016. Rahama Sadau ta ziyarci offishin Cibiyar Wasa na Africa.
Ta haɗu da babban darekta mai suna Ayuko Babu, Darekta na shiri-Asantewa Olatunji, Darekta na gudanar da aiki- Steven Minor, da sauran masu ruwa da tsaki. Babban Manajan na kamfanin watsa shiri (waton One Plus Two Media) Micheal Novak ya halarta a wannan ganawa.
An kafa wannan kamfani na Cibiyar Wasan Kwaikwayo na Africa a shekara 1992 domin ingatar da alʼada na mutanen Afrika da kuma ƙarin fahimtar juna tsakanin mutanen nahiyar Afrika. Wannan Cibiyar Wasan Kwaikwayo yana mayar da hankali akan haƙuri tsakanin mutane masu launin fata daban-daban ta hanyar nune-nunen Fim, zane-zane da kuma ƙerawa.
Tun daga shekara 1992, wannan Cibiyar Wasan Kwaikwayo na Los Angeles yana nunin sabon fim masu kyau, fiye da ɗari da hamsin. Ana nunin masu zane-zane da gwani masu sanaʼa fiye da ɗari daga ƙasar Amirka, Afrika, ƙasar ʼyan Carribean, ƙasar Latin Amirka, Amirka ta kudu, turai, Ƙasashen South Pacific da Canada. Ana yin wannan taro domin nuna banbanci da haɗaddun mutanen waɗanda suke da zuriyarsu a nahiyar Afrika.
ʼYar wasan kwaikwayo Rahama Sadau, tana Los Angeles domin tsayar sabon fim wanda Akon da Jeta Amata suke haɗawa, waton "The American King". Wannan fim zai kawo su ƙasashen Senegal, Afrika ta kudu da Najeriya a cikin watan Disamba.