Advertisement

Gwamnatin jihar Kaduna tayi kashedi ga yan darikar shi'a kan yi wa zaman lafiya barazana

Gwamnati tace zata kama duk wanda ya fito zanga-zanga a jihar karkashin kungiyar Islamic movement of Nigeria
Advertisement

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar cewa baza ta lamunta da ayyukan wasu mabiyan kungiyoyi daya sabawa doka ba ko kuma yake gurbatar da zaman lafiya dake jihar.

Advertisement

A wata takarda da ta fitar ranar litinin wanda kakakin gwamna Samuel Aruwan ya sa hannu, gwamnatin jihar ta fitar da wannan kashedi bayan lamarin da ya faru a jihar Kano kwanan baya tsakanin yan mazhabar shi'a da jami'an tsaro.

Aruwan ya kara da cewa gwamnati ta sanar da jami'an tsaro wajen kawar da duk wani aiki dake neman kawo barazana akan zaman lafiya a jihar.

Kakakin ya sanar cewa gwamnati baza ta amince da duk wani aikin kungiya wanda doka bata san da ita a jihar kuma yayi kira ga jama'a da su kai karar duk wani kungiya dake neman gurbatar da zaman lafiya ga jami'an tsaro.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement