ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

“Na rasa aboki na kut-da-kut wanda ke tare dani cikin zaman lafiya da lokacin riƙici”

Shugaban ƙasa ya bayyana yanda shi da marigayi suke tsakanin juna inda ya ce suna tare cikin walwala da tashin hankali

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari har yanzu yana jimamin tsohon gwamnan jihar Kaduna marigayi AVM Mukhtar Muhammad wanda ya rasu ranar lahadi.

Babban kakakin shugaban Garba shehu yace shugaban ya bayyanar da ƙawazucin sa a wata wasika da ya tura ma gwamnatin jihar Kano da Jigawa.

Yace tawagar gwamnatin tarayya sun kaddamar da wasikar ga gwamnan jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar ranar alhamis.

A cikin wasikar shugaban ya bayyana kyakyawar sanayya dake tsakanin shi da marigayi har ya kira da aboki wanda suke tare cikin halin zaman lafiya har a da lokacin rikici.

ADVERTISEMENT

Kakakin ya sanar da cewa tawagar sun ziyarci jihar Kano inda suka gana da gwamna Abdullahi Ganduje da sarkin Kano Muhammad Sanusi kana suka halarci sallar jana’izar marigayi wanda aka yi cikin dare kasancewa gawar shi ta iso a makare.

Gwamnonin jihohin tare da sarakunan su sun yaba kyakyawan halayyan marigayi kuma sunyi ma shugaban ƙasa godiya da nuna damuwar shi bisa ga rashin da al’ummar jihohin suka yi.

Cikin tawagar gwamnatin tarayya akwai ministan harkar cikin gida Abdurahman Dambazau, Ministan tsaro Mansur Dan-Ali, Ministan ilimi Adamu Adamu da kakakin shugaban kasa Garba Shehu.

Marigayi Mukhtar Muhammad wanda ya rike sarautar “wazirin Dutse” ra rasu a asibiti dake birnin London ranar lahadi 1 ga watan octoba.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT