Wata karuwa mai suna Olubunmi Funke ta shiga hannun hukumar yan sanda na reshin jihar Ogun bisa ga laifin siyar da ɗiyar cikin ta a kan naira dubu dari biyu da tamanin (N280,000) domin ta biya bashin da ake bin ta.
Total media sun ruwaito cewa Funke ta siyar da ɗiyar ga wata Abibat Oyesanya wanda ke cikin wata kungiyar masu safarar yara domin ta biya bashin da ta ciyo.
Banda diyar ta Funke ta saci wasu yara daban wadanda ta hada ta siyar ga yan kungiyar.
Yayyin da take bada amsar laifin da ta aikata, Funke tayi bayani cewa ta koma ga sana'ar karuwanci bayan mijinta ya kore ta daga gidan sa domin ta biya bukatun ta wanda har kungiyar masu safarar yara tare da yin garkuwa da mutane dake yankin yammacin kasar suka gabace ta da siyar da diyar domin shine kadai hanyar da zata iya samu adadin kudin da take nema.
Funke wanda aka gabatar tare da Oyesanya da wata yar kungiyar tace talauci da kunci rayuwa ya sa ta aikata laifin yayin da take amsa tambayoyi a hedkwatar yan sanda na jihar Ogun.
Hukumar yan sanda na jihar sun fara bincike akan yadda za'a gano sauran yan kungiyar kuma tace za'a gabatar da wadanda suka kama a gaban kotu domin samun hukuncin shari'a.