Advertisement

"Mutane na bani mamaki, ni dai babu abun da ya faru dani"-

Yace jita-jitan da ake yadawa na cewa barayi sun shigo gidan sa karya ne domin babu abun da ya faru a gidansa
Advertisement

Fitaccen jarumin kannywood wanda ya shahara a fagen barkwanci Yahaya wanda aka fi sani da Bosho ya musanta labari dake yaduwa na cewa barayi sun haura gidan sa.

Advertisement

Jarumin ya shaida wa wakilin mu cewa babu abun da ya faru a gidan sa kuma shima abun ya bashi mamaki da ya samu labarin.

"Ana ta fadar wannan abun, ni ban san dashi ba, ban san wanda ya fadi haka kuma ban gaya ma kowa ba. Mutane basuwa takaitawa gaskiya. Babu abun da ya faru, nima ina mamakin wannan abun" cewar Jarumin.

Bosho yace yana mamakin yadda mutane ke yada labari mara gaskiya ba tare da sun tabbatar dashi daga wanda labarin ya shafa.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement