Advertisement

Yan Nijeriya baza su sake zaben PDP - inji jam'iyar APC

Wanan ya fito a matsayin raddi ga tsokacin da tsohon gwamnan jihar Imo Achike Udenwa yayi kwannan baya na cewa PDP zata lashe zaben 2019
Advertisement

Jam'iyar APC ta mayar ma jam'iyar adawa ta PDP martani na cewa yan Nijeriya baza su kara zaben PDP .

Advertisement

Wannan martani ne bisa ga tsokacin tsohon gwamnan jihar Imo Achike Udenwa na cewa PDP ce zata samu nasara a zaben 2019.

Jami'in hulda da jama'a na jam'iyar APC reshin jihar Legas Joe Igbokwe ya sanar cewa yan Nijeriya baza su kara amince da mulkin PDP.

Yace " Yan Nijeriya basu koma rayuwar da ba domin yanzu baza a ba kura ajiyar nema game da dukiyoyin kasa. Da na so in mayar ma tsohon gwamna Achike Udenwa martani amma ya kamata ya sani cewa yan Nijeriya sun gano aniyar PDP".

"mun san mai ke faruwa a kasar kuma masu korafin game da gwamnatin yanzu yawanci wadanda suka ci moriyar cin hanci da rashawa na tsohon gwamnatin Goodluck Jonathan ne. Basu ji da dadi ba domin an toshe hanyar samun su".

Advertisement

Kwanan baya shima Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi ma gwamnati mai ci zargi inda yake cewa gwamnatin na karya ne kuma tana yadda jita-jita mara tushe.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement