Advertisement

Ga jerin jaruman kannywood da suka fice cikin shekara 2016

Mun fitar da wannnan sakamokon rawan da suka taka wajen fitowa a fina-finai da suka shahara tare da yanayin kokarin su cikin shekarar bara
Advertisement

Akwai jarumai da suka fice cikin 2016 sanadiyar yanayin yawan fitowar su da kuma yadda fina-finai da suka fito ya samu karbuwa a wajen masoyan fina-finan hausa na masana’antar kannywood.

Advertisement

Wajen fitar da wannan jerin sunayen dandalin finai-finai na Pulse ta hada gwiwa tare da masu sharhi da kuma masoyan fina-finan kannywood.

Ga jerin jarumai 10 da suka fice cikin shekara  2016;

Adam A.Zango

Fina-fina wanda ta shahara  da wannan jarumin ya fito cikin 2016 “basaja gidan yari” da “afra”

Advertisement

Ado Gwanja

wannan jarumin ya shahara wajen fitowa a wasan barkwanci kuma shahara wajen raira waka.

Aisha Aliyu Tsamiya

Jaruma Aisha wanda ta fara fitowa cikin shirin fina-finai cikin shekara 2012 ta samu suna yayin da fito cikin shiri “So” wanda tayi da Adam A.Zango da kuma “Dakin amarya”.

Cikin fina-finai da fito cikin bara sun hada da “Yar mama”, “ Salama”.

Advertisement

Ali Nuhu

Wanda aka yi wa lakabi na “sarkin Kannywood” dan wasan kwaikwayi ne, mai shiryawa kuma mai bada umarni ne na masana’antar fina-finan hausa.

Ya fito cikin shirin “Kasata”, “indon kauye”, “Kisan hutu”.

Fati Shu’uma

Fatima Abubakar wanda aka fi sani da Fati Shu’uma, yar shekara 23 ce wanda ta fara shahara a cikin masana’antar.

Advertisement

Ta fito cikin shirin; “Basma”, “Yar mallam”, “Yan Gambia”.

Jamila Nagudu

Jamila wanda ake wa ikirari na “gimbiyar kannywood” bara fito a shirin fim da dama.

Ta fito cikin shirin “Mahauciya”, “Kaddara ko son zuciya” “Maula”.

Rahama Sadau

Advertisement

Rahama Sadau ta shigo masana’angtar cikin 2013 kuma ta shahara bayan fitowar ta cikin shirin “Gani ga wane” tare da tauraron kannywood Ali Nuhu.

Ta fito cikin shirin; “Ana wata ga wata”, “ Hallacci”.

Sadiq Sani Sadiq

Wannan jarumin ya fara shirya fina-finai kana ya koma ga fitowa da kansa a shirin fim.

Ya fito a cikin “kasata”, “Iyalina”.

Advertisement

Suleiman Bosho

Ya fiye fitowa cikin wasannin barkwanci.

Ya fito cikin shirin “Headmaster”.

Nuhu Abdullahi

Shima Nuhu Abdullahi ya fara shirya fina-finai kana ya koma ga fitowa cikin shirin fim.

Advertisement

Ku kasance tare da domin bayanar da fitattu na bana.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement