Jiya litinin 23 ga watan octoba hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta gabatar da bikin gane gwarzon duniya na 2017.
A taron bikin wanda aka gabatar a birnin London, Crstiano Ronaldo na Real Madrid ya doke Messi da Neymar wajen zama gwarzon shekara.
Ronaldo ya taimaki Real Madrid a kakar bara inda suka zama zakarun nahiyar turai tare da cin kofin La liga.
Wannan shine karo na biyar da dan wasan kasar Portugal ke amsar lambar yabon kuma da wannan yayi kunen doki da abokin gabar sa Messi wanda shima ya amshi lambar sau biyar.
Giroud na Arsenal ya amshi lambar yabo na cin kwallo mafi birgewa a bikin gane gwanaye na duniya wanda aka gabatar a daren ranar litinin.
Kocin Real Madrid Zinedine Zidane shine gwarzon masu horaswa yayin da ita ma Lieke Martens na kasar Holland ta zama gwarzon mata na shekara.
Babban mai tsaron gidan Juventus Gianluigi Buffon shine ya zama gwarzon masu tsaran baya na shekara hakazalika dan kasar Togo Francis kone ya amshi yabo na dan wasa wanda ya aikata abun birgewa na shekara.