Tsohuwar jarumar fina-finan hausa tayi bikin nuna farin cikin karin matsayin da ta samu
Tsohuwar jarumar masana'antar shirya fina-finai hausa na kannywood Fati Muhammad tayi bikin nuna farin ciki da sabon matsayin da ta samu a gidauniyar Atiku Abubakar foundation.
An gabatar da taron bikin a Aso motel dake waff road dake nan garin Kaduna ranar juma'a 20 ga watan octoba.
Fati Muhammad ta shirya walimar domin nuna farin cikin karin matsayin da ta samu a gidauniyar na zama shugaban mata na yankin jihohin arewa maso yamma wanda a da ita ce shugaban mata na jihar kaduna.
Yan uwa da abokan arziki sun taya ta murna ciki har da tsofaffi da sabbin yan fim sun halarci taron bikin domin taya ta murna.
Banda masu ruwa da tsaki na gidauniyar da wasu manyan baki sauran jaruman fina-finan hausa da suka halarci taron sun hada da Abida Muhammad, Wasila Isma'il, Sadiya Gyale, Hauwa Waraka, Fati Yola, Fati KK, Rahma Sirace, Fati Washa, Sakna Gadaz, Hajiya Binta Kofar Soro, Hadiza Kabara da sauransu a bangaren mata.
A bangare maza akwai Rabi'u Rikadawa, Adam A. Zango, Tahir I. Tahir, Abbas Sadik, Jamilu Adamu Kocila, Nasir Koki da dai sauran su.