Advertisement

Gwamna Nasir El-rufai ya samu sarauta yayin bikin sallah

Gwamnan ya samu sarautar Garkuwan talakawa yayin bikin babban sallah a masarautar Jama'a na jihar sa.
Advertisement

Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-rufai ya samu sabon sarautar daga masautar karamar hukumar Jamaa dake jihar.

Advertisement

An nada shi da sarautar "Garkuwan talakawa" ranar bikin babban sallah ranar 21 ga watan Agusta.

Gwamnan ya samu sarautar daga mai martaba sarkin Jama'a Alhaji Muhammed Isa Muhammed jim kadan bayan kammala sallar idi.

Jagoran jihar Kaduna ya gudanar da sallar idin babban sallah a garin Kafanchan na karamar hukumar tare da taya al'ummar garin yin hawan sallah.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya samu sarauta a  kudancin Nijeriya

Advertisement

Sarautar tashi ya biyo bayan wanda takwaransa na jihar Kano ya samu a kudancin Nijeriya.

Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ya samu sarautar Agu Na Eche Mba 1 of Ndigbo wato zaki mai kare hakkin kabilar ibo daga shugaban sarakunan jihar Abia da yan kudu maso gabas Mai martaba Eze Eberechi Dick.

An gudanar da bikin nadin sarautar a fadar sarkin dake Abia ranar alhamis 16 ga watan Agusta. Sarkin Kano Mai martaba Alhaji Muhammad Sanusi na biyu tare da tawagar ma'aikatan gwamnatin jihar Kano da manyan yan siyasar jihar Kano sun halarci bikin nadin sarautar.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement