Advertisement

Sojoji sun kashe yan ta'ada 11 kuma sun gano wajen da suke kera bama-bamai

Kukasheka yace sun gano makamai da dama tare da kunshin kayan hada bam a maboyar yan ta'addar
Advertisement

Rundunar sojojin Nijeriy a ranar laraba ta sanar cewa sojoji sun kashe yan ta'ada 11 kuma sun yi kaca-kaca da inda suke kera bama-bamai a karamar hukumar Ngala dake nan jihar Borno.

Advertisement

Jami'in hulda da jama'a na sojoji Brigediya janar Usman Kukasheka ya sanar da haka a garin Maiduguri.

Kakakin yace rundunar sojoji tare da hadin gwiwan sojojin sama da jami'an JTF sun gabatar da hari ranar talata a maboyan yan ta'ada a shiyar Mogole, Ngaiwa, Tongule, da Warsele dake karamar hukumar Ngala.

Ya fitar cewa sojojin sun fatattaki gurin da yan ta'adan ke hada dabarun su a garin Ngaiwa tare da gano cibiyar hada bama-bamai a garin Tongule.

Babban jami'in soja ya kara da cewa sun kubutar da mutane 86 daga hannun yan ta'adan a kauyukan.

Advertisement

Kukasheka yace sun gano makamai da dama tare da kunshin kayan hada bam a maboyar yan ta'addar.

Sojojin sun gabatar da harin bayan sun samu kwakkwarar labari game da zama yan ta'adan a kauyukan.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement