Advertisement

A kama Shekau cikin kwana 40 a mace ko a raye - umurnin babban hofsan sojin na ƙasa

Chief of Army Staff (COAS), Lt. Gen. Tukur Buratai
Chief of Army Staff (COAS), Lt. Gen. Tukur Buratai
Buratai ya ba kwamandan rundunonin dake yaki da ƙungiyar boko haram a arewa maso gabas umurni na su kama shugaban ‘yan ta’addan
Advertisement

Babban hafsan sojoji na ƙasa janar Yusuf Tukur Buratai ya umurci kwamandan rundunar sojoji na operation lafiya dole na garin maiduguri manjo janar Ibrahim Attahiru da ya kama shugaban ƙungiyar yan ta’adda cikin kwana 40.

Advertisement

A wata bayani da kakakin sojoji na ƙasa birgediya janar Sani Usman ya fitar a daren ranar juma’a, an umurci Attahiru da ya amfani da duk makamai dake tare da rundunar shi wajen kama jagoran ƙungiyar a duk inda yake boyewa.

Usman ya kara da cewa ana neman taimakon sauran ‘yan kasar wajen bada labari da zai taimaka wajen tabbatar da hakan ya faru.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement