Advertisement

Sabuwar cuta ta barke a Kano, ta kashe mutum 8

Rahotanni sun bayyana cewa cutar ta barke ne a makon da ya gabata kuma tuni har ta tayar da hankulan al'ummar garin
Advertisement

Rahotanni sun bayyana cewa cutar ta barke ne a makon da ya gabata kuma tuni har ta tayar da hankulan al'ummar garin.

Advertisement

Wani mazaunin garin mai suna Malam Sulaiman Tafida ya shaida wa manema labarai  cewa cutar ta kashe masa ‘ya’ya uku.

Yana mai cewa  "Ya’yana biyu Umar da Khadija sun rasu a ranakun Juma’a da Asabar, shi kuma Ibrahim a yau ya rasu. Duk irin cuta daya suka yi na dan gajeran lokaci kafin su rasu”.

Tuni dai gwamnatin jihar Kano ta yi gaggawar aika jami'an ta zuwa kauyen domin tabbatar da gaskiyar cutar.

Kwamishinan lafiya na jihar, Kabiru Getso shi ya sanar da haka ta baki jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya, Isma’il Gwammaja a jiya Talata.

Advertisement

Ya ce da zarar sun kammala bincike game da lamarin, za su sanar da jama’a sakamakon

Advertisement
Latest Videos
Advertisement