Advertisement

Barayin shanu 700 sun tuba, sun mika makamai ga jami'an tsaro

Kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar ASP Aliyu Mukhtar ya tabbatar da hakan inda  ya ce kimanin mutane 700 ne na daga cikin masu satar shanu da sace-sace suka tuba
Advertisement

Kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar ASP Aliyu Mukhtar ya tabbatar da hakan inda  ya ce kimanin mutane 700 ne na daga cikin masu satar shanu da sace-sace suka tuba.

Advertisement

A bisa rahoton da BBC ta fitar, rundunar ta kuma ce daruruwan 'yan ta'adar, ciki har da masu garkuwa da mutane sun tuba kuma sun ajiye makamansu.

Yan fashi suna addabar jama'ar jihar har ma da wasu jihohi dake makwabtaka da Kaduna.

Hakan ya faru ne bayan rantsuwa da suka sha da alkawarin cewa ba zasu koma cutar da jama'a ba.

Rundunar dai ta ce za ta ci gaba da bibiyar wadannan mutanen don tabbatar da tuban su.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement